Dandalin ismail2029 {bincike a cikin alqur'ani}

WANE AIKI NE YAFI ALKHAIRI?
Daga Abi zarri cewa an tambayi Annabi (SAW)
wane aikine yafi alkhairi? Sai yace :"Yin imani
da Allah da kuma jihadi don daukaka kalmar
Allah" sai aka tambaye shi game da 'yanta
bayi fa? Sai yace: "Wanda yafi tsada kuma
yafi amfanarwa ga 'yan uwansa" sai aka ce
masa idan na kasa yin wannan aikin fa? Sai
yace: "Ka taimakawa wanda ya rasa wani
abunsa, ko ka yi alkhari ga wanda gidansa ya
rushe" sai aka ce masa idan na kasa fa? Sai
yace "Kada ka yiwa mutane sharri don hakan
ma sadaka ce da ka bayar ga kanka". [Adabul
Mufrad Hadith 305]