filin wasa kwakwalwa na pride fm radio gusau

MAI YASA
-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-
BA'A KARBAN
-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\-\
ADDU'OIN MU
-\-\-\-\- _______ -\-\-\-\-\-\ _____
Bada minti 2 wajen karantawa
watarana Malam Ibrahim Dan Adhama yana tafiya a
birnin basara, sai mutane suka taru a wajensa,
sukace dashi
mai yasa muna addu'a amma ba'a amsa mana
gashi kuma Allah Subhanahu wata'ala yace:
kurokeni zan amsa muku?
Sai yace dasu yaku mutanen Basara, Zukatanku
summutu sakamakon sakamakon
sabani abubuwa goma (10) shiyasa kuke addu'a
kuji shiru
= = = = = = = = = = = = =
Na Daya: Kunsan Allah subhanahu wata'ala, amma
bakwabasa hakkinsa
Na Biyu: Kuna da'awar son Annabi Saw, amma
kunyi watsi da sunnarsa.
Na uku: Kunkaranta Al-kur'ani mai girma, amma
bakwa aiki dashi.
Na Hudu: Kuna da'awar kuna gaba da shedan
amma kunayi masa biyayya.
Na Biyar: Kuna fatan shiga Aljannah amma bakwa
aiki dominta.
Na Shida: Kuna tsoran shiga Wuta amma kuna jefa
kanku acikinta.
Na Bakwai: Kunce mutuwa gaskiyace amma bakuyi
shiriba.
Na Takwas: Kunshagala da laifukan wasu bakwa
ganin naku Laifin.
Na Tara: Kuna binne matattu kullum amma bakwa
daukar Izna.
Na Goma: Kuna shan Ni'imar Allah bakwa
godemasa.
Allah kasa mugyara.