JIBWIS SOCIAL MEDIA NASARAWA STATE CHAPTER

Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 17,094 cikin As-Sunanul
Kubraa, da athari na 7,441 cikin
Shu'abul Iman cewa Sayyidina Umar Bin Khattab Allah Ya
kara masa yarda a lokacin da ya zo mutuwa
ya yi wa jama'a magana ya ce: ((Ku sani, mutane ba za su
gushe ba suna cikin alheri matukar dai
shugabanninsu sun kyautatu)). Har yanzu shi Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 17,095
cikin As-Sunanul Kubraa, da athari na 7,442
cikin Shu'abul Iman daga Al-Qaasim Bin Mu'khai'mirah cewa
wannan babban Taabi'ii ya ce:
((Zamaninku shi ne mai mulkinku, idan mai mulkinku ya yi
kayu sai zamaninku ya yi kyau, idan mai
mulkinku ya lalace sai zamaninku ya lalace)).