DANDALIN MUTANEN SHARADA KANO.

DUKKAN RAYUWARMU ADDINICE!(1)
Muna neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa.
Dasunan Allah mai rahama mai jinkai.
Godiya ta tabbata ga Allah,tsira da aminci sukara tabbata ga Annabinmu Muhammad(s.a.w)da ahalinsa da sahabbansa da wadanda suka shiriya da shiriyarsa.
Bayan haka;
Hakika bayan soyayyar Ubangiji(s.w.t)da Manzonsa(s.a.w)yana wajaba soyayyar masoya Allah da kiyayya ga makiyansa.
Yana daga cikin AKIDATUL-ISLAMIYYA(Akida ta musulunci)Lallai yana wajaba ga kowane musulmi yayi Addininsa da wannan Akidar,haka kuma yaso masoyinta yakuma ki makiyanta yaso ma'abota TAUHID da IKLASI(Masu kadaita Allah da tsarkakeshi)yayi biyya ga abinda sukebi.
Haka kuma yayi kiyayya ga ma'abota SHIRKA(Masu hada Allah da wani wajan bauta)ya kuma yi tawaye ga abinda sukebi.
Hakan yana daga cikin Tafarkin Annabi Ibrahim(A.s.)da wadanda suke tare dashi,wadanda aka Umarcemu da muyi koyi dasu ta inda ubangiji(s.w.t)yake cewa a cikin qur'ani;
''HAKIKA YA KASANCE A GAREKU ABIN KOYI MAI KYAU DANGANE DA IBRAHIM DA WANDA SUKE TARE DASHI LOKACIN DA SUKE CEWA DA MUTANENSU LALLAIMU MUN BARRANTA DAGA GAREKU DA ABINDA KUKE BAUTAWA WANDA BA ALLAHBA MUNKAFIRCE MUKU,KUMA KIYAYYA DA GABA TAFARA TSAKANINMU DAKU HAR ABADA HARSAI KUNYI IMANI DA ALLAH SHI KADAI'' (S.Mumtahana Aya ta 4)
Haka abin yake cikin Addinin Annabi Muhammad(s.a.w)ta inda Ubangiji(s.w.t)yake cewa;
''YAKU WADANDA KUKAI IMANI KADA KU RIKI YAHUDU DA NASARA MASOYA,SASHINSU MASU SON SASHINE,DUK WANDA YA SOSU DAGA CIKINKU HAKIKA YANA TARE DASU,HAKIKA ALLAH BAYA SHIRYARDA MUTANEN DA SUKE AZZALUMAI''(S.Ma'ida Aya ta 51)
Ya ''yan uwana masu girma,wannanfa ana maganane akan haramcin soyayya ga Ahlul kitab(mabiya littafi)kadai,amma dangane da haramcin so ko biyayya ga kafirai gabadayansu ma'ana ko wane irin kafirine koma a ina yake Ubangiji(s.w.t)yana cewa;
''YAKU WADANDA KUKAI IMANI KADA KU RIKI MAKIYANA DA MAKIYANKU MASOYA''(S.Mumtahana Aya ta 1)
Hakika Allah ya haramtawa Mumunai soyayyar kafirai koda kuwa kafirannan sunkasance mafiya kusanci a garesu ta fuskar Nasaba,Ubangiji(s.w.t)yana cewa;
''YAAKU WADANDA KUKAI IMANI KADA KU RIKI IYAYENKU DA ''YAN UWANKU MASOYA INDAI SUNASON KAFIRCI ABISA IMANI,DUK WANDA YASOSU DAGA CIKINKU WADANNAN SUNE AZZALUMAI''(S.Tauba Aya ta 23)
Ubangiji ya karacewa a wata ayar daban ba wannanba;
''BAZAKA SAMU WASU MUTANEBA WANDA SUKAI IMANI DA ALLAH DA RANAR KARSHE,SUNA SOYAYYA GA MAKIYA ALLAH DA MANZONSA,KODA SUN KASANCE IYAYENSUNE KO 'YA'YANSU KO 'YAN UWANSU KO JAMA'ARSU(DANGINSU).............''(S.Mujadala Aya ta 22).
Hakika ayau dayawan mutane sun jahilci wannan Asali mai girma,ta inda zaka samu wasu daga mutane suna cewa wai Yahudu ko Nasara 'yan uwanmune!
Lallai wannan hatsarine babba kalmace mai girma da zakaji shuwaga banni ko wasu daga malamai suna furtata,wanda kuma babu wanda zai baka wani dalili na Aya ko Hadisi ko ingantattun maganganun magabata na Musulunci.
Komenene aka haramta a addini zakaga an maye gurbinsa da wani kamar yadda aka Haramtamana soyayya ga kafirai sai aka maye gurbin hakan da soyayya ga Muminai a Akida ta Musulunci,ta inda Ubangiji(s.w.t)yake cewa;
''LALLAI MASOYANKU ALLAH DA MANZONSA DA WADANDA SUKAI IMANI,SUNE SUKE TSAIDA SALLAH SUKE BADA ZAKKA KUMA SUNA RUKU'U*DUK WANDA YABI(YASO)ALLAH DA MANZONSA DA WADANDA SUKAI IMANI,TO HAKIKA RUNDUNAR UBANGIJI SUNE MASU RINJAYE''(S.Ma'ida Aya ta 55-56)
Ubangiji yafada awata ayar;
''MUHAMMAD MANZON ALLAHNE,DA WADANDA SUKE TARE DASHI(SAHABBAI)MASU TSANANINE AKAN KAFIRAI,MASU RAHAMANE A TSAKANINSU..........''(S.Fathi Aya ta 29)
Cikin Suratul Hujurat Aya ta 10;
''HAKIKA MUMINAI 'YAN UWAN JUNANE,KUYI SULHU A TSAKANIN 'YAN UWANKU,KUJI TSORAN ALLAH KO AI MUKU RAHAMA''
Mumini dan uwan Muminine ko wanene ko kuma a ina yake indai Muminine,Muminai 'yan uwan junane a Addini da Akida ta Musulunci shine Al-kitab was-Sunnah(Qur'ani da Hadisi)koda Nasabarsu ta banbanta,ko Garuruwansu(mazaunansu)ko zamunansu.zamu gane hakan idan muka koma Fadin Allah(s.w.t);
''DA WADANDA SUKAZO DAGA BAYANSU SUKE CEWA YA UBANGIJI KAIMANA GAFARA DA 'YAN UWANMU WADANDA SUKA RIGAYEMU YIN IMANI KADA KASA WANI GILLI(RIKO)A ZUCIYOYINMU DANGANE DA WADANDA SUKAI IMANI YA UBANGIJINMU LALLAI KAI MAI TAUSASAWANE MAI JINKAI''(S.Hashri Aya ta 10).
Da wannan zamu gane cewa muminai tun daga na farko harzuwa na karshe 'yan uwanjunane,masoyan junane,sashinsu masu yiwa sashi Addu'ane,masu nemawa juna gafarane.
Dan haka ya 'yan uwana masu girma muyi taka tsan-tsan wajan Furta magana komai kankantarta,Musamman ayanzu da Muke tsamo-tsamo a bagauniya da hauma-hauma ta SIYASA har wasu daga wawaye acikinmu suke ware siyasa daban Addini daban bayan kuma mu rayuwarmu dukkanta Addinice kuma shine gatanmu,wallahi idan babau Addini akowane Motsinmu a rayuwa,to lalle wannan rayuwar bazatai amfaniba ballantana tayi dadi.
Muhadu a kaso na gaba na wannan sakon dayake da alaka da Rayuwarmu.
SUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA ASHHADU ALLA ILAHA ILLA ANTA ASTAGFIRUKA WA ATUBU ILAIK.