VOC & TEC IKCOE CHAPTER DUTSINMA KATSINA STATE DEPARTMENT OF AGRIC EDU

SAKO DAGA ZAUREN FIQHU
***********************
Assalamu alaikum Jama'ar Musulmi!! Muna kira da babbar murya zuwa gareku cewa DON GIRMAN ALLAH ku dena yin Uploading din Hotunan zanen 'batancin nan wanda Jaridar Faransa tayi ma Musulunci!! Duk wanda yayi Uploading ko Tagging din irin wadannan Hotunan, WALLAHI shima ya taimaka wajen mutuncin Annabinmu (saww) kuma WALLAHI Allah ba zai kyaleshi ba shima. Kar ku manta cewa tun azamanin Manzon Allah (saww) an samu Kafiran Mawakan Larabawa wadanda suka rika rubuta wakoki suna ZAGIN MANZON ALLAH (saww) suna cin mutuncin addininsa, amma Mai yasa yanzu babu irin wakokin, kuma bamu da labarin irn miyagun kalmomin da sukayi amfani dasu?? AMSA: Saboda Sahabban da akayi abun azamaninsu, sun danne abun basu ci gaba da watsa ma duniya ba. Koda Tabi'ai basu ga irin wadannan Wakokin ba. Sai dai labarin kawai. Kuma sunyi hakane don Girmama Manzon Allah (saww). Don haka muma bai kamata mu rika nuna ma wanda bai gani ba ya gani!!! Don Allah jama'a ku tayamu wajen isar da wannan sanarwar ta hanyar sharing a facebook da whatsapp da twitter da sauransu. Bissalam.