Kallah ! Innaha Muhibbah...Jama'atu Ahbabu Rasulullah,Sokoto chapter

JAHILCI KO SON ZUCIYA
BISIMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
WASSALATU WASSALAM ALA RASULILLAHI. WA ALIHI WA SAHBIHI WA AZWAJIHI WA ZURRIYATIH. سلام.على من.اتبع الهدى A dukkanin al'amuran addini da ma na rayuwa dole ne ka yarda na Annabi s a w shine mafi a'ala.
Dalilin dayasa nayi wannan magana shine lura da yanda abubuwa suke wakana a yanzu.
Bansan me ya kawo hakan ba tsakanin jahilci ko son zuciya. Wannan kira ne ga Duk wani Dan dariqar tijjaniyya ko qadiriyya cewa kayi ruqo da dukkan abun da ya tabbata daga manzon Allah s a w kuma ka fara gabatar dashi kafin na shehun ka.
Mu dauki salati da farko.
Allah a cikin alqurani yayi umarni ga muminai sun dinga yin salati ga annabi Muhammad saw.
{إن الله وملائكته يصلون على النبي يا أيها الذين آمنوا صلوا عليه وسلموا تسليما} [الأحزاب: 56]. Al'adar sahbban annabi s a w ce a Duk sanda aka saukar da wahayi dake umarni da yin wani aiki sai sun tambayeshi yaya zasu aikata.
Da suka tambayeshi s a w yaya zasuyi salati sai ya Dan yi jinkiri sannan ya amsa musu da cewa su dinga yin salatil ibrahimiyya. Ga matanin hadisan
Cikin Riyadusaalihina #1405- وعن أبي محمد كعب بن عجرة رضي الله عنه قال: خرج علينا النبي صلى الله عليه وسلم فقلنا: يا رسول الله قد علمنا كيف نسلم عليك، فكيف نصلي عليك؟ قال: ((قولوا: اللهم صل على محمد، وعلى آل محمد، كما صليت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد. اللهم بارك على محمد، وعلى آل محمد، كما باركت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد)). متفق عليه.
قوله: (قد علمنا كيف نسلم عليك)، أي: بما علمهم في التشهد من قولهم: السلام عليك أيها النبي ورحمة الله وبركاته. ............. Yaya zamuyi salati a gareka? Sai manzon Allah s a w yace: kuce: allahumma salli ala Muhammad, wa ala aali Muhammad kama sallaita ala aali Ibrahim .................. Da hadisi mai lamba #1406 cikin riyadussalihina - وعن أبي مسعود البدري رضي الله عنه قال: أتانا رسول الله صلى الله عليه وسلم ونحن في مجلس سعد بن عبادة رضي الله عنه، فقال له بشير بن سعد: أمرنا الله تعالى أن نصلي عليك يا رسول الله، فكيف نصلي عليك؟ فسكت رسول الله صلى الله عليه وسلم حتى تمنينا أنه لم يسأله، ثم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: ((قولوا: اللهم صل على محمد، وعلى آل محمد، كما صليت على آل إبراهيم، وبارك على محمد وعلى آل محمد، كما باركت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، والسلام كما قد علمتم)). رواه مسلم.
قوله: ((كما صليت على إبراهيم)). ((وكما باركت على إبراهيم)). وقع للبخاري في كتاب: أحاديث الأنبياء في ترجمة إبراهيم عليه السلام، من حديث كعب بن عجرة بلفظ: ((كما صليت على إبراهيم، وعلى آل إبراهيم)). وكذا قوله: ((كما باركت)). .................. Bashiiru Dan naziiru yace da manzon Allah, Allah ya umarcemu da muyi salati a gareka ya rasulallahi, yaya zamuyi salati a gareka?
Sai manzon.Allah s a w yayi Shiru har sai da sukaji Dama basu tambayeshi ba. Sannan manzon Allah s a w yace. Kuce:"allahumma salli ala Muhammad wa ala aali Muhammad .........zuwa qarshe. Da hadisi na #1407- وعن أبي حميد الساعدي رضي الله عنه قال: قالوا: يا رسول الله كيف نصلي عليك؟ قال: ((قولوا: اللهم صل على محمد، وعلى أزواجه وذريته، كما صليت على آل إبراهيم، وبارك على محمد، وعلى أزواجه وذريته، كما باركت على آل إبراهيم إنك حميد مجيد)). متفق عليه.
قوله: ((وعلى أزواجه)). زوجاته صلى الله عليه وسلم: إحدى عشرة، توفي منهن اثنتان على عهده، ومات عن تسع.
((وذريته))، أي: جميع أولاده، وبناته، وذريتهن. Amma a yanzu abin mamakin shine yadda wasu ke kauda kai ga barin na manzon Allah s a w suna fifita na shehunnansu akan na kowa. Wannan kuskure ne. Bawai ina kore ingantuwar na shehunnan ba Bal ina nuna kuskuran a gabatar dasu kafin na manzon Allah s a w. Mu dawo kan zikiri.
Zikiri yana daga ibadar da Allah ya umarci musulmai da su kasance suna yawaita Shi har ma yayi alqawarin gafara da rabo mai girma ga ma'abotansa. ..........والذاكرين الله كثيرا والذاكرات أعد الله لهم مغفرة و أجرا عظيما. ...........الآية Kuma Alhamdulillah ruwayoyi Sunzo mabanbanta suna nuna irin zikiran da manzon Allah yayi ya kuma koyarda sahabbansa. Dan me zan gabatar da wani Zikirin kafin na Annabi.
Da zikiril amfass da Hallarar bandiri, da mi'adi da sauran zikiran qadiriyya Duk suna bayan tasbihi da istigfari da hailalar da manzon Allah ya koyar. Haka diwani, zikirin dukan qirji da ragowar zikiran tijjaniyya basu kai na manzon Allah s a w daraja ba kuma na manzon Allah ya kamata a gabatar. Kada fa ku manta shehunnan nan na Annabi suka riqa har suka kai wannan matsayi Dan me zaka watsar da na Annabi ka kama na wani.
Ina qara jaddadawa ba wai ina kore ingancin na shehunnan ba. Bal ina ganin kuskure ne a gabatar dasu akan na ma'aiki s a w.
Abinda ya jawo wannan yan tunasarwa shine maganganun da suka fito daga wasu yanuwa yan dariqa na ganin cewa ai Duk wani Zikiri Idan ba na shehunsu ba to bai da daraja kuma yin riqo dashi a saki nasu kuskure ne.
Wannan bai kamata ba. Kuma bai ma halatta musulmi na kwarai ya dinga raya hakan a ransa. Shiyasa mu yan ashabul kahfee qarqashin jagorancin maulana shaikh Dr abduljabbar sheikh Dr nasir kabara (amirul wa'izina) muke da wani Abu guda daya.
Muna gabatar da farilla ne kafin mandubi. Wanda hakan shine aula da kowanne Dan dariqa.
Amma maimakon a yi riqo da igiyar sai ake qoqarin ganin an jefeta da Duk irin qazantar da aka ga Dama. Kuma Allah cikin ikonsa sai ya haramta nasara ga ma'abota hakan.
Ita dai gaskiya daya ce rak. Daga qinta kuma sai bata. Muna rokon Allah s w t ya tsarkake zuqatanmu bisa ga iklasi da kuma kyakyawar niyya. Ya Bamu Ikon kwaikwaya dukkanin abinda manzon Allah yayi da kuma yin aiki da dukkanin abun da ya fada Dan alfarmar sayyadissaadaati.
Amin. Nine naku
Aliyu Assufiy Algambiawiy
Ashabul kahfee warraqeem kano Nigeria