DANDALIN MASOYA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI

SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI Yana
Cewa:-
"Mu 'Yan Tijjaniyya Mugode Ma ALLAH
Yayi Mana Dukkan Alkhairai To Amma
Fa Babban Abinda Yake Gabanmu
Shine Kiyayewa, Samun Tariqah Dabam
Kiyayewa Dabam, Domin Tafiyarmu
Yafi Nakowa Hatsari Domin Idan
Mutum Yana Kan Keke Ya Fadi Sai Ace
Ya Baka Ji Ciwo Ba Idan Kuwa Kana
Mashin Ne Sai Kayi Hatsari Sai a
Tambaya Ba Karaya Ko?? Idan a
Motane Kayi Hatsari Sai Ace Ya Ba
Mutuwa Ko??? Idan Kuma Kana Jirgin
Sama Kayi Hatsari Sai Dai Ace Yana
Ciki ALLAH Ya Jikansa, To Mu Yan
Tijjaniyya Tafiyarmu a Jirgi Take
Saboda Haka Sai Mun Tsaya Da
Gasken Gaske".
SHEHU YANA MAGANA NE AKAN
WASU DA SUKE SA RIGAR 'DARIQA
WAI SU 'YAN HAQIQA YA CE:"KO INA
MUKA GANSU MU GUJE SU, BA WAI
ANA MAGANAR SU 'YAN 'DARIQA NE
KO A'A, SHI KANSA MUSULUNCINMA
YA KORE SU DON WANDA YACE
SHEHU ALLAH NE(Wa'iyazubill ah), KO
YAKE KETA HADDIN SHARI'A AI YA
QARYATA MANZON ALLAH(S.A.W) DA
QUR'ANI MAI GIRMA KACOKAM
KUNGA KENAN YA FADO A JIRGIN
SAMA BA'A MA MAGANARSA TASHI TA
QARE".
MUN GODE SHEHU!
ALLAH YA QARAWA SHEHU LAFIYA
DA JURIYA YA KARESHI DAGA
SHARRIN MAQIYA, ALLAH KA KARE
MANA IMANINMU AMEEEEN.