Wasa kwakwalwa (Addini da al'amuran Duniya) na Aramma Namas

AN TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA.
..
Baka taba yin kuka ba sanda
kake cire ran dan Adam?
- Sai ya amsa, nayi kuka sau daya,
nayi dariya sau daya, kuma naji tsoro sau daya..
- Ubangiji yace: Menene yabaka
dariya..?
sai yace wani mutum ne naje
daukan ransa, shi kuma yana
fadawa mai dinka masa takalmi... kayishi mai kyau yanda zanyi
shekara ina sawa, sai na dauki
ransa ba tare da yasa takalmin
ba...
-Ubangiji yace:menene yasaka
kuka? yace sanda ka aikeni dauko ran
matarnan a sahara, bayan ta haifi
danta a lokacin sai nayi kuka
saboda ihun da dan yakeyi ba
mai taimakonshi...
-Ubangiji yace: Menene yabaka tsoro?
yace sanda ka aikeni in dauko
ran wani malami, duk sanda
nakusanci dakinsa haskene yake
dawo dani, hasken ransa ya
tsoratar dani sanda nazo cireshi... -UBANGIJI YACE MASA KASAN WAYE
WANNAN MALAMIN..
.???YACE A'A....
-Yace wannan yaronne daka
dauki ran mahaifiyarsa a sahara,
Ni Na jibinci lamarinsa ban barshi a hannun kowa ba....!!!
ALLAHU AKBAR.
.
Dan uwa ko yar uwa mu mika
lamurranmu wurin ubangiji.
Ya zama majibincin lamarinmu, dan shi zai wadatamu da komi a
rayuwa. ALLAH ya taimake mu
AMEEN